Posts

Showing posts with the label Siyasa

Firaministan Pakistan ya tsallake rijiya da baya

Image
  Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya tsallake rijiya da baya, bayan da ‘yan majalisar kasar suka kada kuri’ar yanke kauna, yayin da sauran kungiyoyin fararen hula suka matsa kan a fara shirin gudanar da babban zaben kasar.  Sharif ya sami kuri’un amincewa guda 180, yayin da ‘yan majalisa 172 suka nuna rashin amincewa da salon shugabancin sa, abinda ya bashi damar ci gaba da rike mukamin sa da kyar.  Ko da yake jawabi, kakakin majalisar dokokin kasar Raja Pervais Asharf, yace a yanzu abinda majalisar zata mayar da hankakli shine batun babban zaben da ke tafe.  Sharif wanda ya gaji Imran Khan ya yabawa mambobin jam’iyyyar sa da ke majalisar bayan da suka amince da salón mulkin sa, tare da yanke hukuncin sake bashi dama, ta hanyar kada kuri’ar amincewa da shi.  rfi

Yau Ake Rufe Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Image
  Daga karfe 12 na daren yau Alhamis 23 ga Fabrairu, 2023, za a fure yakin neman zaben ’yan takarar shugaban kasa da Majalisun Tarayya da za a gudanar ranar Asabar. Dokar Zaben Najeriya ta haramta yin duk wani nau’in yakin neman zabe ko tallata dan takara daga sa’a 24 kafin ranar zabe. A yayin rubuta wannan rahoton, kusan awa 12 ya rage wa daukacin jam’iyyu da ’yan takara su yi duk abin da za su iya, su kuma rufe yakin neman zabensu, sannan a fafata a akwatunan zabe a ranar Asabar. Jam’iyyu 18 ne ke zawarcin kujerar shugaban kasa bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu a ranar 29 ga watan Mayu. Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan ne a mazabu 1,491 da ke kananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zabe 176, 846. ’Yan Najeriya ne za su yi alkalanci a zaben mai mutum miliyan 95.5 da suka yanki katin zabe, wadanda akasarinsu matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35, ko da yake kawo yanzu babu alkaluman adadin wadanda suka karbi katin zabensu. Many

Yan sanda a jihar Kano sun kame 'yan daban siyasa fiye da 60

Image
‘Yan sanda a jihar Kano sun sanar da kame ‘yan daban siyasa akalla 61 yayin wani sumame da suka kaddamar a kokarin kakkabe barazanar rashin tsaro da aikata laifukan da ke ci gaba da tsananta a sassan jihar. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Mamman Dauda da ke bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ya rabawa manema labarai, ya ce matakin kame ‘yan daban umarni ne daga babban sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali-Baba. A cewar sanarwar galibin kamen an yi shi ne yayin gangamin siyasar da ke ci gaba da gudana a sassan jihar, a wani yunkuri na dakile barazanar ‘yan daban dai dai lokacin da babban zaben Najeriya ke ci gaba da karatowa. A Sanarwar da gidan Rediyon Faransa (RFI) ya wallafa a shafinsa, ta bayyana cewa ta hanyar tsaftace gari daga barazanar ‘yan daban siyasa ne kadai za a iya samun damar tafiyar da harkokin zaben da ke tunakarowa a wata mai zuwa. Rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta ce ta gudanar da sumame ranar 4 ga wat