Buhari Zai Sayo Motocin Sulke 400 Don Tsaron Su Abuja
Shugaba Buhari ya amince da sayo motocin sulke guda 400 don amfani da su wajen tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya da jihohin Nasarawa da kuma Neja. Sabon Kwamandan Rundunar Tsar Birgediya, Manjo-Janar Mohammed Usman ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a jawabin godiyarsa a bikin nada masa anininsa bayan karin girma da ya samu. Shugaban kasa tare da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da uwargidan kwamandan, Dokta Rekiya Usman, ne suka nada masa aninin. Jim kadan bayan kammala bikin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, shugaban kasa ya bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in da yake yi wa kasa hidima. Ya yaba wa Janar Usman bisa jajircewarsa da rikon amana da hakuri da kuma kwazo. Buhari, a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba wa iyalan kwamandan bisa hakurin da suka yi na jure kalubalen da ya fuskanta wajen gudanar da aikinsa. A nasa jawabin, Manjo-Janar Usman, ya gode wa shugaban kasa bisa irin gagarumin goyon bayan da ya bai wa Rundunar