Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya yi sabon Aure
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu Hauwa'u Adamu Abdullahi Dikko a Kano ranar Juma'a.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa an gudanar da daurin auren ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nasarawa GRA a cikin babban birnin tarayya.
Sannan kuma Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin a lokacin daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance waliyin amarya.