Posts

Showing posts with the label Hakar ma'adinai

Gwamnatin Kano Ta Umarci Shugabannin Kananan Hukumomi Su Rinka Kai Rahoton Duk Wuri Da Ake Hakar Kasa Ko Yashi Ba Bisa Ka'ida Ba

Image
Kwamishinan ma'aikatar kasa da tsare-tsare ta jahar Kano, Alhaji Abduljabbar Mohammed Umar ya bayyana hakan ga manema labarai bayan karbar koken al'ummomin kananan hukumomiin Gezawa da Gaya da Bebeji da Dawakin Tofa, akan yadda ake hakar kasa a yankunansu ba bisa ka'ida ba. Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Kano ta lura  da cewa wasu kamfanoni da suke hakar kasa a garuruwan Chediya Ingawa da Kalebawa a karamar hukumar Dawakin Tofa, wanda gwamnati ta basu umarnin dakatawa, da hakar kasar sun dawo sun ci gaba da aikin hakar kasar bisa zargin suna samun goyon baya daga sama. Abduljabbar ya kuma kara da cewa a doka gwamnatin Tarayya ita ta ke bada izinin hakar kasa ko ma"adanai, haka kuma Dokar ta baiwa Gwamnatin Jaha ikon sahalewa tare da izinin Gwamna, da izinin shugaban karamar hukuma, da kuma al'ummomin garuruwan da abin zai shafa. Kwamishinan ya kuma zayyano sharudan da doka ta tanadar kafin fara aikin hakar kasa ko ma'adanai. ...