NAHCON Ta Gargadi Jama'a Kan Yada Labaran Karya Na Daukar Aiki
Wannan sanarwa ce daga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) na fadakar da alhazai musulmi masu niyyar zuwa aikin Hajji, da masu neman aikin likita ko duk wani mai sha’awa game da yadda ake yada sakonnin bogi dangane da daukar aiki a tawagar likitocin NAHCON. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin yada labarai da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace labari ya riski hukumar cewa ana yada bayanan karya ga daidaikun mutane da ke ikirarin daukar ma’aikata na dundundun a NAHCON ko a matsayin mambobin tawagar likitoci da sauran mambobin kwamitin aikin Hajji. A halin yanzu NAHCON ba ta daukar ma’aikata na dundundun , ko wasu ma’aikata a kan haka da duk wani sakon da ke nuni da cewa karya ne. Sahihan tsarin aikace-aikacen tawagar likitocin Hajji ana gudanar da shi ne ta hanyar shafin hukumar na yanar gizo kuma har yanzu tana ci gaba. Hukumar ta bukaci jama’a da su yi watsi da duk wata hanyar sadarwa ta daban, su dogara ne kawai da bayanai daga t...