Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Taya Sanata Kwankwaso Murnar Sallah, Tare Da .Yabawa Da Kyawawan Halayensa Na Shugabanci
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yiwa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyarsa ta NNPP Injiniya Rabi'u Kwankwaso barka da Sallah a lokacin da ya hada kai da dubban magoya bayan Kwankwasiyya domin yi wa shugaban kasa mubayi'a a wani bangare na gudanar da bukukuwan Sallah. A sanarwar da mai rikon mukamin babban sakataren yada labaran gwaman, Hisham Habib ya sanyawa hannu, Ta Ce, Gwamna Yusuf ya ce shugaban da ya yi gwamnan jihar har sau biyu ya na yi wa mutane da yawa jagoranci kuma ya kasance abin koyi a jihar da kuma yankin Arewa. A lokacin da yake jawabi a wajen bikin da magoya bayansa suka shirya, gwamnan ya ce shugaban wanda yay Gwamna har sau biyu, ya jagoranci ci gaba rayuwar mutane da dama Ya godewa Sanata Kwankwaso bisa nasiharsa ta uba da kuma ka’idojinsa na karfafa mutane. Mawaka da dama ne suka baje kolin fasaharsu a wajen taron tunawa da ranar a gidan Sanata Kwankwaso tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NNPP. B...