Posts

Showing posts with the label Renewed Hope

NAHCON Ta Bayyana Manyan Nasarori Da Ta Cimma a Ayyukan Hajji a Zamanin Gwamnatin Renewed Hope

Image
Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin gwamnatin Renewed Hope ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, tare da tabbatar da cewa jin daɗin maniyyata na ci gaba da kasancewa a sahun gaba. Farfesa Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma a Katsina, inda ya yi cikakken bayani kan gyare-gyare da matakan da aka ɗauka wajen inganta gudanar da aikin Hajji a Najeriya. A cewarsa, duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, hukumar tare da goyon bayan shugaban ƙasa, ta aiwatar da muhimman matakai da suka tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2024 tare da kawo sauƙi ga maniyyatan Najeriya. Shugaban hukumar ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya amince da naira biliyan 90 domin rage tasirin hauhawar darajar kuɗin waje a kuɗaɗen aikin Hajjin 2024, da kuma ƙarin naira biliyan 24 domin biyan bashin da ya rage daga kamfanonin jiragen sama na 20...