Posts

Showing posts with the label Abdulmumin Jibrin Kofa

Ban Ce Na Goyi Bayan Kudirin Gyaran Dokar Haraji Dari Bisa Dari Ba: Ina Bada Hakuri Kan Rashin Fahimta - Abdulmumin Jibrin Kofa

Image
Ina jan hankalin al'ummar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji, Jihar Kano, Arewa da Nigeria cewa BABU WURIN DA KO SAU ƊAYA NA CE INA GOYON BAYAN SABABBIN DOKOKIN HARAJI ƊARI BISA ƊARI.  Abin da nace, akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Nigeria. Kuma mu yan Majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da mu ke da shi a majalisa, mu tsaya daram mu goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin. Mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu ko mu gyarata a yadda ba za ta cutar da mu ba.  Kuma mu yi amfani da wannan damar dokar da aka kawo mu bijiro da wasu sabbi da muka tabbatar za su amfani Arewa, domin a shigar da su a cikin kundin ƙudirorin. A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nigeria adalci a tsarin dokar. Amma ra'ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.  A matsayi na na mai hawa huɗu a Majalisa, ban taba kuma ba zan taɓa goyo...