Posts

Showing posts with the label Naja’atu

Naja’atu Muhammad Ta Bayyana Dalilin Ficewa Daga Jam’iyyar APC

Image
Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kasar yayin da Babban Zabe ya karato. Hajiya Naja’atu ta sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga Janairun 2023, wadda ta aike wa Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu. ’Yan sanda sun yi ajalin wani mutum a Kano Wainar da aka toya a haduwar ‘karshe’ tsakanin Messi da Ronaldo Naja’atu wadda yanzu haka Kwamishina ce a Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda a Najeriya, ta ce kalubalen da kasar nan ke fuskanta a yanzu ya sanya dole ta fito daga takunkumin duk wata jam’iyya don ta shiga gwagwarmayar kai kasar nan zuwa tudun tsira. A wata sanarwa da fitar a wannan Asabar din, Naja’atu ta ce duk jam’iyyyu a fadin kasar nan ba su da wani bambancin akida. Ta bayyana ta cewa jam’iyyun kasar kamar tufafi mabanbanta da ’yan siyasa sukan saka don wata bukata ta kansu kebantacciya. ’Yar siyasar ta ce ta mayar da hankali wurin goyon bayan jama