Posts

Showing posts with the label AHMSP

AHMSP Tayi Martani Ga Rahoton Da Ba A Tabbatar Ba Kan Shugaban NAHCON, Ta Bukaci Jaridu Su Daina Wallafa Labaran Karya

Image
Kungiyar Ƙwararrun ‘Yan Jarida Masu Tallafawa Aikin Haji (AHMSP) ta yi watsi da rahoton da wata kafar labarai, News Point Nigeria, ta wallafa a ranar 14 ga Oktoba, 2025, karkashin jagorancin edita Mista Farouq Abbas, wanda ya shafi ofishin Shugaban Hukumar Kula da Haji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman. AHMSP ta bayyana cewa rahoton cike yake da bayanan da ba a tabbatar da su ba, tare da nuna son zuciya da rashin bin ka’idojin aikin jarida, wanda hakan ke iya gurbata sahihancin aikin labarai musamman a fagen da ya shafi Hajj da Umrah. A cewar kungiyar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman yana gudanar da ayyukansa cikin gaskiya, doka, da tsari, ba tare da wani laifi ko take haddi ba. Dukkan ayyukan hukumar daga rabon ma’aikata, gyaran farashin Hajj, har zuwa gudanar da ayyuka suna tafiya ne bisa tsarin NAHCON da doka ta tanada. Kungiyar ta bayyana cewa “ikrarorin rashin gaskiya” da rahoton ya bayar ba su da hujjar da za ta tabbatar da su. Haka kuma, ta ce bai dace ka...