INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da mako ɗaya
Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris INEC ta tabbatar wa da BBC ɗage zaɓen, bayan wani taron sirri da manyan jami'an hukumar suka yi a Abuja. Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita na’urar tantance masu zaɓe ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabirairu. Sun ƙara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin zaɓen shugaban ƙasar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba. Tun da farko, an tsara gudanar da zaɓen ne a ranar asabar 11 ga watan Maris. Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan wata kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta amince da buƙatar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sake saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS wadda aka yi am...