Posts

Showing posts with the label kasuwa

Sai Buhari Ya Yi Magana Za Mu Karbi Tsohon Kudi —’Yan Kasuwa

Image
  ’Yan kasuwa a wasu yankunan Najeriya sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun N5oo da N1,000 har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce su fara karba. ’Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, a washgarin da bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN). Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci. Harkoki sun fara kankama a Kano Wani tan kasuwa a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Adamu Hamza, ya ce sun fara samun karuwar ciniki,  “tsakanin jiya (Talata) da yau (Laraba), kudi ya fara yawo a hannun jama’a, suna kawowa kuma muna karba.” Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar Talata injinan ATM a birnin Kano suka fara bayar da tsoffin kudin, sai dai yawanci N500 ne....