Posts

Showing posts with the label Habasha

Air Peace Zai Kwaso Daliban Najeriya Da Suka Makale A Sudan Kyauta

Image
  Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce zai kwaso daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan inda yaki ya barke, kyauta zuwa gida. Rikicin shugabanci ya kazance a Sudan a baya-bayan nan, har ta kai ga rufe sararin samaniyar kasar. Akalla daliban Najeriya 5,000 da ke Sudan sun nuna matukar bukatar a dawo da su gida, inda wasu daga cikinsu ke kokarin tsallaka iyaka zuwa kasar Habasha, mai makwabtaka da Sudan. Shugaban kamfanin Ake Peace, llen Onyema, ya sanar da cewa idan ’yan Najeriya da ke Sudan za su iya tsallaka iyaka zuwa kasashen makwabtakan Sudan, to kamfaninsa zai kwaso su zuwa gida a kyauta. Ya ce aikin kwaso su ya wuce a bar wa gwamnati ita kadai, saboda bai kamata a yi asarar dan Najeriya ko daya ba a rikicin na Sudan. Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin ranar Talata za ta fara kwaso ’yan Najeriyan ta kasar Habasha. Wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce Ma’aikatarta Harkokin Kasashen Waje na aiki da gwamantin kasar Habasha, domin amfani da sara