Search This Blog

Showing posts with label Wike. Show all posts
Showing posts with label Wike. Show all posts

Thursday, 2 November 2023

Wike Yayi Alkawarin Kammala Gyaran Masallacin Kasa Da Cibiyar Yada Addinin Kirista Kan Lokaci

Mista Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), ya yi alkawarin tabbatar da kammala aikin gyaran Masallacin kasa da cibiyar Kiristoci ta kasa da ke Abuja kan lokaci.

Wike ya ba da wannan tabbacin ne bayan ya duba aikin gyaran manyan gine-ginen kasa guda biyu a Abuja ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ta tuno da cewa, shugabannin Masallacin kasa da Cibiyar Ibadar Kirista sun ziyarci Wike tare da rokon a kammala ayyukan gyara.

Wike, bayan ya tabbatar musu da cikakken goyon bayansa, ya yi alkawarin ziyartar cibiyoyin biyu domin ganin al'amura da kansa kafin ya yanke shawara kan mataki na gaba.

Ministan ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan kammala rangadin aikin da aka gudanar a Masallacin kasa saboda karin aikin da ya kamata a yi.

Ya nuna jin dadinsa da abin da aka yi ya zuwa yanzu, ya kuma ba da izinin a saki kudi ga dan kwangilar domin samun damar kammala aikin.

A cibiyar kiristoci ta kasa, Wike ya ce zai duba kudin aikin gyaran kashi na biyu kuma zai amince da shi idan yana cikin abin da FCT za ta iya bayarwa.

Ya ce idan har kudin ya zarce matakin amincewa da babban birnin tarayya Abuja, zai tunkari Shugaba Bola Tinubu domin ya amince masa, inda ya tabbatar da cewa Tinubu ba zai yi watsi da irin wadannan muhimman abubuwan tarihi na kasa ba.

“Ba ya gaba da kowane addini; ya dauki dukkan addini a matsayin daya, domin mu Najeriya daya ce,” inji shi. (NAN)

Sunday, 27 August 2023

Kada Wanda Ya Kafa Allunan Taya Ni Murnar Zama Minista – Wike

 


Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya hana karkafa duk wasu allunan talla da nufin taya shi murnar zama Minista.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na ma’aikatar, Anthony Ogunleye, Wike ya ce ya yanke shawarar daukar matakin ne saboda nuna kishin kasa da kuma mayar da hankali wajen aikin da Tinubu ya sa shi.

Sanarwar ta ce Ministan ya gode da fatan alherin, amma ya bukaci a dakatar da amfani da irin wadannan allunan tallan.

Wike ya ce babban burinsa shi ne ya bunkasa Abuja ta yadda mazauna cikinta za su ji dadin zamanta a zamanin mulkinsa.

Ya kuma ce ya yana matukar girmamawa da kuma mutunta bukatun mazauna birnin tare da jajircewa wajen ganin ya biya musu su.
AMINIYA

Wednesday, 23 August 2023

Sunayen Unguwannin Da Wike Zai Yi Rusau A Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince a rusa gine-gine sama da 6,000 a yankunan Garki da Jabi da wasu unguwanni 28 da suka saɓa da tsarin birnin tarayyan ba.

Hukumar kula da birnin tarayyar (FCTA) ta fitar da jerin sunayen unguwannin, inda ta bayyana cewa gine-ginen ta riga aka sanya wa alama ne rusau din zai shafa, a shirin gwamnati na kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a birnin.

Ga jerin unguwannin da abin zai shafa:

Apo Mechanic Village
Byanzhin.
Dawaki.
Dai Dai.
Durumi.
Dutse.
Garki.
Garki Village.
Gishiri.
Gwagwalada.
Idu.
Jabi.
Kauyen Kado.
Karmo.
Karshi.
Karu.
Katampe.
Kauyen Ketti.
Kpaduma.
Kabusa.
Kauyen Kpana.
Kubwa.
Lokogoma.
Lugbe.
Mabushi.
Mpape.
Nyanya.
Piya Kasa.
Jikwoyi
Galadima
Tun ranar Litinin da aka rantsar da tsohon gwamnan na jihar Ribas a matsayin Minista, ya sha alwashin dawo da birnin kan ainihin taswirarsa, ruguza gine-ginen aka yi ba bisa tsaru ba, da kuma kawo karshen badaƙalar filaye a babban birnin.

Wike wanda ya ce ya zaga birnin Abuja a cikin dare domin ya ga al’amura da kansa, ya koka bisa yadda aka yi gine-gine a filayen da gwamnati ta kebe ba don ginawa ba.

Ya ce: “Za mu kwace duk filayen da masu su ba su gina ba, don haka dole masu su su ci gaba da aiki nan take.

Sai dai daraktan sashen kula da ci gaban FCTA, Muktar Galadima ya ce za a gudanar da wani sabon bincike.

(AMINIYA) 



Tuesday, 15 August 2023

Wike Ya Ziyarci Ganduje A Ofishin APC

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, wanda aka tantance domin zama minista, Nyeson Wike, ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Umar Ganduje a ofishin jam’iyyar.

Ganduja ya karbi bakuncin Wike a ofishinsa ne yayin da ake rade-radin yana shirin sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC. Sai dai ya sha musanta shirin komawa jam’iyyar mai mulki.


Wike wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC ya mika sunansa a cikin jerin ministocin da zai nada ya fito karara ya yaki dan takarar shugaban kasan PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar.

A yayin wani bikin da aka shirya masa bayan ya mika mulki ga zababben gwaman jiharsa, Simi Fubara, an ji gwamnan na rokon Wike kada ya yi watsi da shi idan ya dawo jam’iyya mai mulki.


Rade-radin komawar Wike jam’iyyar APC sun kara karfi ne bayan Shugaba Tinubu ya mika sunansa a jerin ministocinsa.

Shugabannin PDP dai sun bayyana rashin jin dadinsu, tare da kurarin daukar mataki a kan tsohon gwamnan na Ribas.
(AMINIYA)


Wednesday, 3 May 2023

Wike Ya Bawa Ma'aikata Hutu Domin Tarbar Tinibu A Ribas

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu domin tarbar zaben shugaban kasa, Bola Tinudu a ziyarar da zai kai jihar.

Wike, wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne da ke takun saka da dan takarar shguaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, ya ce yayin ziyarar aikin ta kwana biyu, Tinubu zai kaddamar da gadar sama da ginin zamani da ya gina wa kottun Majistare a birnin Fatakwal, hedikwatar jihar.

DAGA LARABA: Yadda Iyaye Ke Kashewa ’Ya’yansu Aure A Arewa
La Liga: Barcelona ta yi wa Osasuna gida da waje a bana
Wike wanda ya juya wa Atiku baya a zaben da Tinubu ya lashe, ya ce, “Ina kira ga daukacin al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwato su yi wa zabebban shugaban kasarmu kuma abin alfaharimu, Mai Girma Sanata Bola Ahmed Tinubu gagarumar tarba, tare da bayyana abin da aka san su da shi na karamci yayin a ziyarar da zai kaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da za su zama tarihi.

“Saboda haka na ayyana ranar Laraba, 3 ga Mayu 2023, a matsayin ranar hutu domin muane su samu damar fita su yi wa zababben shugaban kasa maraba.

“Hakazalika daga karfe 8 na safe zuwa 3 na yinin ranar shaguna da wuraren kasuwanci da ke kan titin Rumuola zuwa Rumuokwuta a Karamar Hukumar Obio/Akpor za su kasance a rufe.

“Saboda haka ina kira ga kungiyoyin kwadago da hukumomin tsaro su ba da hadin kai su kuma tabbatar da wannan umarni,” in ji Gwamnan Wike, a jawabinsa ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa tun a lokacin ziyarar Tinubu na yakin neman zabe a jihar, ya nuna sha’awarsa ta gayyatar sa domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar

Bayan kammaala zaben kuma ya aika wa zababben shugaban kasan goron gayyata, kuma ya amsa cewa a jihar zai fara  kai ziyarar aikinsa ta farko bayan zabe.

AMINIYA /NAD 




Wednesday, 11 January 2023

Almundahanar N96bn: Wike Ya Sake Maka Amaechi A Kotu

Gwamnatin Ribas ta shigar da sabuwar kara kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96.

An maka Amaechi tare da Tonye Cole, dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar bisa zargin sayar da kadarorin jihar.

HOTUNA: Masaukin Ronaldo da burwarsa a Saudiyya
DAGA LARABA: Dalilin Da Maza Ke Tsoron Auren Mata ’Yan Boko 
Zacchaeus Adangor, babban lauyan Gwamnatin Jihar Ribas, ya tabbatar da shigar da karar.

Nyesom Wike, gwamnan Ribas, ya kafa wani kwamitin mutum bakwai don bincikar Amaechi kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna.
Kwamitin ya kuma binciki batutuwan da suka shafi sayar da kadarorin da tsohon gwamnan ya yi.

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a 2015 kan binciken, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa.

A ranar 27 ga Mayu, 2022, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kansa.

Sakamakon haka ne, Wike, ya umarci babban lauyan jihar da ya gurfanar da tsohon gwamnan tare da Tonye Cole da wasu mutum biyar da ake zargin na da hannu a badakalar.

Wike ya kuma umarci a shigar kan kamfanin Sahara Energy, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen satar kudaden.

A watan Oktoban 2022, Okogbule Gbasam, Alkalin Babbar Kotun Jihar Ribas, ya dakatar da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnati mai ci ke bincike kan gwamnatocin da suka shude ba, kan zargin cire makudan kudade ba bisa ka’ida ba.

A wasu lokuta ana zargin siyasa a cikin lamarin, da nufin daukar fansa musamman idan ya kasance akwai adawa a tsakan

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...