Posts

Showing posts with the label Hajji

Karin Kudin Tikiti: Za A Dauki Dala 100 Daga Guzurin Alhazai

Image
  Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce za ta dauki Dala 100 daga cikin kudin guzurin maniyyata aikin Hajjin bana, domin biyan karin kudin kujera da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar su suka yi.  Yakin da ake yi a Sudan ya sa kasar rufe sararin samaniyarta, don haka dole sai jiragen da za su dauki maniyyatan su bi sabuwar hanya da ta bi ta kasar Chadi da Habasha da Eretiyiya da Kamaru kafin isa kasar Saudiyya. ِKafin barkewar yakin da ya sa aka rufe sararin samaniyyan Sudan, jiragen maniyyatan Najeriya kan tsallaka ne ta Chadi su shiga Sudan ne kadai kafin su isa Saudiyya. Wani manaja a wani kamfanin da zai yi jigilar alhazan ya bayyana wa Aminiya cewa, “A duk lokacin da aka tsayin tafiya ya karu to dole kudi su karu saboda man da za a zuba a jirgi ya karu, haka kuma kudin da za a biya ma’aikatan jirgi shi ma ya karu; Hakan ya janyo dole a yi kari a kudin tikitin alhazan.” Bayan yamutsa gashin baki da kai-kawo a tsakanin Hukumar NAHCON da kamfanonin jiragen a kan karin kudin,

An Bawa Tsoho Dan Kasar Pakistan Da Ya Kwashe Shekaru 15 Yana Tara Kudin Aikin Umrah Kyautar Kujerar Hajji

Image
Wani dattijo dan kasar Pakistan da ya fito a cikin wani faifan bidiyo a lokacin da yake fitowa daga Madina ya lashe zukatan miliyoyin al’ummar musulmin duniya saboda sanye da kaya mai sauki ba tare da takalmi a fuskarsu ba a lokacin da suke fitowa daga masallacin Annabi a watan Ramadan. A wani al’amari da ba a saba gani ba, faifan bidiyon mutumin ya yadu a kafafen sada zumunta inda mutane ke nuna soyayyar su ga saukin kayan sa da kuma alaka da yanayin da ake gani a fuskarsa yayin da daya ke barin Masallatan Harami guda biyu. An ce mutumin wanda ya fito daga Pakistan, makiyayi ne da ya tara isassun kudade sama da shekaru 15 don yin aikin Umrah. Wannan shaharar da ya yi ba zato ba tsammani ta sa a yanzu ya samu kyautar Hajji da Umrah da dama daga Saudiyya da Pakistan da dama ciki har da abin da ma'aikatar nishadantarwa Turki Al Sheikh ya bayyana a Twitter. IHR

Mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022- Saudia

Image
Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta ce kimanin mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wannan adadin a cewar ma’aikatar ya hada da baki su miliyan hudun da suka samu izinin shiga kasar domin Hajjin Umarah. Kamfanin dillancin labarai na SPA ya rawaito a ranar Alhamis cewar, Ma’aikatar ta yi amfani da harsuna 14 wajen isar da muhiman bayanai da suka shafi addini da kiwon lafiya da sauransu ga maniyyatan yayin zamansu a kasar. Kazalika, ta ce ta tabbatar da maniyyatan sun samu kulawar da ta dace wajen gudanar da harkokinsu da suka hada yanka da ziyartar wurare da sauransu. Ta kara da cewa, ta sahale wa masu rike da biza daban-daban ibadar Umarah a wannan shekarar. Ta ce a 2022 ne ta kyale masu bizar yawon shakatawa suka yi Umarah yayin zamansu a kasar, wanda hakan shi ne karon farko da irin hakan ta faru.