Mun himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudurinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin tsaron Kano a wani taron buda baki a gidan gwamnati da ke Kano. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin. A cikin sanarwar, gwamnan ya yabawa jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan kasa, tare da sanin irin gudunmawar da suke bayarwa. Gwamna Yusuf ya nanata jajircewar gwamnatin sa wajen karfafa tsarin tsaro domin isar da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummar Kano ke sa ran yadda ya kamata. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta fara siyan kayan abinci domin rabawa, inda jami’an tsaro na cikin wadanda suka ci gajiyar shirin. Bugu da kari, ya yabawa gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu bisa amincewa da rabon kayan abinci da za a raba ga marasa galihu a...