An faɗa mana ƙarasa ayyukan da wasu suka faro babbar nasara ce - Zaɓaɓɓun gwamnoni
An faɗa wa zaɓaɓɓun gwamnonin da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya, cewa a cikin nasarar shugabanci, akwai ƙarasa ayyukan da magabatansu, suka faro. Matakin zai taimaka wajen tabbatar ci gaban ƙasa da alkinta dukiyar al'umma da rage kashe kuɗi wajen gudanar da harkokin mulki a matakan jihohi. Wannan jan hankalin, na cikin ɗumbin bayanai da shawarwari da aka gabatar wa zaɓaɓɓun gwamnonin Najeriya, yayin wani taron sanin makamar aiki da aka shirya musu a babban birnin ƙasar, Abuja. Manufar taron na kwana uku, ita ce shirya gwamnonin masu jiran gado da dabaru da hikimomin shugabanci kafin a rantsar da su nan da kwana 12. Ƙungiyar gwamnoni ta Najeriya ce ta shirya taron a Abuja, inda ta gayyato ƙwararru a fannoni daban-daban game da sanin dabarun shugabanci a ciki da wajen ƙasar domin bunƙasa ƙwarewar sabbin gwamnonin. Jiga-jigan 'yan siyasa kamar Simon Lalong na jihar Filato da Nasiru El-rufa'i da su Kayode Fayemi sun ja hankalin zaɓaɓɓun gwamnonin da za su hau ...