Gwamnatin Kebbi ta bullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin saukaka musu yin wahalar noma a jihar.
Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farrfado da aikin noma domin jihar ta cigaba da rike kambunta a bangaren noman shinkafa a Nijeriya.
Saboda haka ne ta gina karamin wurin noma na zamani a kananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta.
Wannnan a cewarsa, kari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin.
(AMINIYA)