Posts

Showing posts with the label Gwamnan Bankin

Emeifele Ya Sake Kaiwa Buhari Ziyara A Sirrance

Image
  Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin  Emefiele, ya shiga bayan labule tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Aso Villa da ke Abuja. Bayanai sun ce wannan dai ita ce ziyara ta biyu kuma cikin sirri da Gwamnan Babban Bankin Kasar ya kai wa Shugaba Buhari tun bayan dawowarsa Najeriya a ranar 12 ga watan Janairu. Wannan ziyara na zuwa ne bayan Emefiele ya halarci taron Bankin Bunkasa Tattalin Arziki na Daular Larabawa wanda Darekta Janar na bankin, Dokta Sidi Ould Tah ya jagoranta a ranar Alhamis. Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo bayan da aka rika rade-radin cewa jami’an tsaron na sirri na nemansa ruwa a jallo. A makonnin bayan nan ne dai Emefiele ya bar kasar biyo bayan binciken wasu zarge-zarge da ake yi masa, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma samar da kudade ga ayyukan ta’addanci. Sai dai tuni CBN ya kore wannan zargi yana mai cewa Emefiele ya ketare kasar nan saboda dalilai na hutun karshen sheka