Abin Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi Na Biyu)
Datti Assalafiy✍️ Mutane biyu ne sukayi sanadiyyar yakin da ya barke a Kasar Sudan, kuma Musulmai ne abokan juna na kut da kut. Na farko sunansa: General Abdel Fattah al-Burha, shine Shugaban Sojojin Sudan wanda ya jagoranci kifar da mulkin tsohon shugaba Umar Al-Bashir ya haye kujeran mulki Na biyu sunansa: Janar Muhammad Hamdan Dagalo (Hemetti), shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine babban Kwamandan rundinar tsaro na agajin gaggawa da ake kira Rapid Support Forces (RSF) Wanene Dagalo? Kamar yadda na fada a sama, yanzu haka Dagalo shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine Babban Kwamandan RSF, wato yana rike da matsayi guda biyu a Sudan kenan Rapid Support Forces (RSF) rundinace ta tsaro da aka kafata tun a lokacin yakin basasar da akayi a yankin Dafur na Kasar Sudan, suna aiki da sarrafa makaman yaki kamar sojoji Janar Muhammad Hamdan Dagalo gawurtaccen dan ta'adda ne, kuma dan tawaye, a lokaci guda kuma dan siyasa, kamar dai misali da a nan...