Yanzu-Yanzu: Nasiru Gawuna Ya Taya Abba Gida-gida Murnar Lashe zaɓen Gwamnan Kano
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kuma wanda ya yiwa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ya karɓi Kaddarar faɗuwa zaɓe tare da taya Abba Kabiru Yusuf Murnar lashe zaɓen gwamnan Kano. Nasiru Gawuna ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da yayi bayani na tsawon mintuna biyu, wanda Sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24. ” Mun tsammaci Hukumar Zabe INEC zata duba koken da mukai mata na samun kura-kurai a sakamakon zaben da ya gudana, amma a yau 29 ga watan maris ta sake tabbatar da matsayar ta ta hanyar mikawa Abba Kabiru Yusuf Shaidar lashe zabe , don haka mun dauki wannan a matsayin kaddara”. Inji Gawuna Yace dama ya fada a baya cewa zai karɓi Kaddara idan ya fadi zaben don haka yayi kira ga magoya bayan sa da dukkanin al’ummar jihar kano da zu baiwa sabon zaɓaɓɓen gwamnan hadin kai don ya gudanar da mulkin sa cikin kwanciyar hankali da lumana. Mataimakin Gwamnan ya kuma yi addu’ar Alla...