Hukumar NAHCON Ta Koka Bisa Yadda Wasu Jahohi Suka Ki Bawa Maniyyatan Da Suka Biya Kudinsu Ta Bankin Ja'iz Kujerunsu
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da yadda aka ki ba wa maniyyatan da suka yi rajista ta tsarin adashin gata mai dogon Zango na Bankin Ja'iz kujerun su wanda a sakamakon haka suka fuskanci matsaloli a wasu jihohi kamar Kaduna da Abuja da Gombe da Jigawa. A cewar sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na hukumar alhazai ta kasa, wadannan Jihohin dai sun alakanta wannan matakin da NAHCON da Bankin Jaiz ya yi na kin mika kudaden ga Hukumomin Jihohi a kan lokaci. Muna bayyana sarai cewa irin wadannan uzuri ba su da tushe balle makama. Yana da kyau a fayyace cewa Bankin Jaiz ya yi gaggawar tura kudin adashin gata mai dogon Zango zuwa jahohin tun kafin fara aikin Hajjin bana. Hakan ya faru ne tun kafin da yawa daga hukumomin alhazai na jihohi su biya. Na biyu, a yawan tuntubar da muka yi da jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihohi, an yanke shawarar cewa rabon da ake baiwa alhazai ya kai kashi 60/40 bisa 100 ga mani...