Posts

Showing posts with the label Satar waya

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kotunan Tafi Da Gidanka Domin Magance Satar Waya

Image
Gwamnan jihar Kano, Yusuf Abba, ya amince da kafa kotunan tafi da gidanka domin tabbatar da hukunta masu satar wayar a jihar cikin gaggawa. A wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Alhaji Bature Tofa ya fitar, ya ce kotunan tafi da gidanka za su hada hannu da rundunar hadin gwiwa ta musamman domin hukunta wadanda aka kama. Yusuf ya ce manyan titunan birnin sun haska ne bayan shafe shekaru takwas na duhu yayin da aka kashe fitulun. “Mayar da fitilun kan titi na cikin kokarin da sabuwar gwamnati ke yi na magance matsalar fashi da makami da sace-sacen waya da sauran miyagun ayyuka, musamman a babban birnin Kano. "Aikin da ake ci gaba da gudanarwa ya fara tun ranar Talata kuma zai ci gaba har sai an kubutar da kowane bangare na jihar daga duhun da ke ba da mafaka ga masu aikata laifuka da 'yan bangar siyasa," in ji shi.

An Sace Wayar Sanata A Taron Karbar Shaidar Cin Zabe

Image
  Sanata Orji Uzor Kalu ya ce an sace masa wayar hannu a lokacin taron mika takardar shaidar cin zabe ga zababbun ’yan majalisar dokoki ta tarayya. Orji Kalu wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Abiya, ya sanar da haka ne tare da jan hankalin mutane cewa su yi hattara da duk wanda zai yi magana da su ta lambobin wayarsa. Ya ce, “An sace wayata mai dauke da lambobina na MTN da Glo  a lokacin taron mika takardar shaidar cin zabe da ya gudana a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Kasa da ke Abuja “Na sanar da kamfanonin sadarwa amma duk wanda ke da bayanin da zai taimaka, muna bukata,” in ji shi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook. Uzor Kalu ya lashe zaben Sanatan Abia ta Arewa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, karkashin inuwar jam’iyyar APC. A ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu, Hukumar Zabe ta Kasa ta mika wa ’yan majalisar da suka ci zaben takardar shaidar nasara a zaben.