Barrister Muhuyi Ya Bukaci A Samar Da Sashen Yaki Da Cin A Ma'aikatar Kasa Ta Kano
Muhuyi Magaji ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan da sauran ma’aikatan ma’aikatar a ziyarar ban girma da suka kai ofishin sa. A sanarwar da mai taimakawa Muhuyin kan harkokin yada labarai ta kafar sadarwa ta zamani, Nura Ahmed, ya ce Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa wanda ya jaddada wannan bukatar gaggawar, ya ce ta hanyar daukar irin wannan matakin ma’aikatar za ta gudanar da ayyukanta ba tare da kalubalen ayyukan cin hanci da rashawa ba kuma za ta tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin ma’aikatar. Shugaban wanda ya nuna jin dadinsa ga kwamishinan bisa ziyarar ta farko da ya kai masa, duk da haka ya yaba masa bisa bullo da wasu tsare-tsare da nufin inganta ayyukan hidima a ma’aikatar. Ya shaidawa kwamishinan cewa, sama da kashi sittin cikin dari na shari’o’in da ke hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa na da alaka da filaye, ya kara da cewa matakin da Kwamishinan ya dauka a halin yanzu zai kawo saukin ayyukan hukumar ta wann...