Posts

Showing posts with the label Asibitin Sir Sunusi

Gwamna Abba Kabir Ya Bada Umurnin Gaggauta Gyaran Babban Asibitin Sir Sanusi

Image
A kokarinsa na tabbatar da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya masu sauki a jihar kamar yadda yake kunshe a cikin tsarinsa na yakin neman zabe na 2023, gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta gyara babban Asibitin Sir Sanusi. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Gwamnan ya bayyana haka ne a ziyarar ba-zata da ya kai asibitin wanda ya kasance daya daga cikin al’adun Gwamnan na aikin sa ido. Gwamnan wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda asibitin ke tabarbarewa ya yi alkawarin cewa za a fara aikin gyare-gyaren ne da gaske domin tabbatar da cewa majinyata da ma’aikatan lafiya sun samu yanayin da ya dace domin isar da ingantaccen kulawa a asibitin. "Dole ne in gaya muku, abin da na gani da kaina yana da ban tsoro ga idona, ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatinmu za ta kawo muku agaji nan da nan bayan wannan ziyarar." “Zan umurci ma’aikatar lafiya da dukkan...