Posts

Showing posts with the label Burodi

An samu cimma matsaya tsakanin Kungiyar Masu Gidajen Burodi da Hukumar Karbar Korafe-Korafe

Image
Gwamnatin Jihar Kano da Kungiyar masu hada Burodi ta jihar Kano sun cimma matsaya akan farashin Burodi a jihar. Wannan na zuwa ne bayan da farashin buhun Fulawa ya sauka a Najeriya zuwa naira dubu 60 daga sama da naira dubu 80,saidai ba’a ga saukin farashin Burodi a jihar Kano da sauran jihohin Najeriya ba. Amma a madadin gwamnatin Kano, hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano tayi wani zama na musamman da Kungiyar masu Burodi domin cimma matsaya akan rage Burodin. A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taronta da kungiyar masu yin burodi a ranar Laraba, hukumar ta karbar korafe korafe ta bayyana cewa, duk da faduwar farashin buhun Fulawa amma farashin Burodi bai sauya ba. A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun hadin gwiwa da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ta Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado da kuma shugaban kungiyar masu yin burodin Alhaji Jibrin Hamza da sakataren Kungiyar, sun amince cewa ba zasu rage farashin Burodin ba...