Posts

Showing posts with the label Wa'adi

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Image
  Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi. Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja. Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba. El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara. Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu. Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye. El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki. Ya kara da cewar shugaban gama

Zan mayar da Wa'adin Sakamakon JAMB Shekara 4 - Sanata Kwankwaso

Image
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin tsawaita wa’adin sakamakon jarabawar shiga jami’a (JAMB) zuwa shekaru hudu idan ya ci zaben shugaban kasa. Majiyarmu ta rawaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Bauchi, lokacin da yake mika tutoci ga ’yan takarar gwamna shida da na Majalisar Dattijai 18 na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ranar Alhamis. An yi garkuwa da DPO a Filato Yadda aka yi wa Sakkwatawa kisan gilla a Anambra Kwankwaso ya ce dalibai da dama na samun sakamako mai kyau a rubuta jarabawar karo na farko, amma da zarar sun rasa gurbi a jami’a sai sun sake sabon lale bayan ba laifinsu ba ne. “Babu gaira babu dalili an sanya daliban da iyayensu lalubo kudin zana jarrabawa na shekaru biyu koma fiye. Haka ne ya sanya muku ga dacewar sauya haka. “Haka kuma za mu kirkiri sabuwar dokar dakatar da jarabawar JAMB din na tsawon shekaru hudu, domin ’ya’yanmu su yi amfani da sakamakon wajen samun gurbin karatu a manyan makarantun a w