Posts

Showing posts with the label Titi

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Bayyana Gamsuwar Da Yadda Aikin Titin Karkashin Kasa Da Gadar Sama A Tul'udu Da Dan Agundi Ke Gudana

Image
Daga Naziru Idris Ya'u Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake gudanar da ayyukan Tal'udu da DanAgundi na karkashin kasa da gadar sama. Gwamnan wanda aka gan shi cikin farin ciki a lokacin da ya kai ziyarar bazata inda ya yaba da irin ci gaban da aka samu kawo yanzu. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, Sanatan Kano ta kudu Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila, da ‘yan majalisar zartarwa, ya kai ziyarar duba ayyukan da ake gudanarwa. Gwamnan ya mika godiyarsa ga ‘yan kwangilar aikin tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati ta jajirce wajen ganin an kammala wadannan ayyuka a kan lokaci da kuma inganci. Ya kuma kara jaddada cewa abin da gwamnati ta sa a gaba shi ne walwala da ci gaban al’ummar jihar Kano. Ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayansa da dama wadanda suka daga hannu don nuna godiya da ayyukan da ake gudanarwa. Gagarumin nuna goyon baya

Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Aikin Gadar Sama Mai Musayar Hannu Kan Naira Biliyan 15 A Kano

Image
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin samar da gadar sama musayar hannu kan kudi Naira biliyan 15 a kofar Dan'agundi da ke cikin birnin Kano a wani bangare na hangen nesa na inganta zirga-zirgar ababen hawa a tsohon birnin. Gwamnan wanda ya ziyarci wurin da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tare da wasu mambobin majalisar zartarwa, ya tabbatar da ganin gwamnatinsa na ganin an mayar da tsakiyar birnin zuwa matsayin babban birni. Za a iya tunawa cewa Gwamna Yusuf a watan Disamba, 2023, ya ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin na biliyoyin nairori tare da umarnin kammalawa watanni goma sha takwas.  An bayar da wannan ayyuka da yawa tare da wata gadar musanyar hannu a shataletalen  Tal'du kuma a cikin tsakiyar gari, don sauÆ™aÆ™a cunkoson ababen hawa. "Mun kirkiro hanyoyin da za a iya amfani da su kuma ana sa ran masu ababen hawa za su bi ka'idoji don kare lafiya tare da ba da damar gudanar da aikin yadda ya kamata." Gwamna Abba Kabir ya kuma aza h