Posts

Showing posts with the label Karfafa Dangantaka

Gwamnatin Kano Ta Nemi Karfafa Dangantaka Tsakaninta Da Kasar Saudi Arabia

Image
Gwamnatin jihar Kano ta nuna sha’awarta na karfafa alakar da ke tsakaninta da kasar Saudiyya domin amfanin gwamnatocin kasashen biyu. A cewar sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan batu ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamin jakadan Saudiyya a Kano,  Khalid Ahmad Al-adamawi tare da kodinetan kungiyar musulmi ta duniya Dr Salisu Ismaila a gidan gwamnati. Gwamnan ya yaba da ziyarar tare da neman karin tallafin karatu da gwamnatin Saudiyya ke baiwa ‘yan asalin Kano don yin karatu ko kuma ci gaba da karatunsu a jami’o’in Saudiyya. Alh Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da addu'ar Allah ya tabbatar da burinsa na kafa Jami'ar Kiwon Lafiya da Asibitin koyarwa domin shiri ne wanda a cewar Gwamnan zai dauki nauyin kula da lafiyar jama'a da dama a Kano da Jihohi makwabta da sauran su. Ya kuma nemi tallafi ta fannin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da rage mace-macen mata...