Posts

Showing posts with the label YAKI

Abin Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi Na Biyu)

Image
Datti Assalafiy✍️ Mutane biyu ne sukayi sanadiyyar yakin da ya barke a Kasar Sudan, kuma Musulmai ne abokan juna na kut da kut. Na farko sunansa: General Abdel Fattah al-Burha, shine Shugaban Sojojin Sudan wanda ya jagoranci kifar da mulkin tsohon shugaba Umar Al-Bashir ya haye kujeran mulki Na biyu sunansa: Janar Muhammad Hamdan Dagalo (Hemetti), shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine babban Kwamandan rundinar tsaro na agajin gaggawa da ake kira Rapid Support Forces (RSF) Wanene Dagalo?  Kamar yadda na fada a sama, yanzu haka Dagalo shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine Babban Kwamandan RSF, wato yana rike da matsayi guda biyu a Sudan kenan  Rapid Support Forces (RSF) rundinace ta tsaro da aka kafata tun a lokacin yakin basasar da akayi a yankin Dafur na Kasar Sudan, suna aiki da sarrafa makaman yaki kamar sojoji Janar Muhammad Hamdan Dagalo gawurtaccen dan ta'adda ne, kuma dan tawaye, a lokaci guda kuma dan siyasa, kamar dai misali da a nan Nige

Abun Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi na daya) - Datti Assalafiy

Image
Datti Assalafiy✍️ Shimfida: Akwai taba addini a yakin Sudan, saboda shi tsohon shugaban Kasar Sudan Umar Albashir wanda aka masa tawaye aka hambarar dashi da karfin tsiya ya bawa Musulunci kariya sosai a Sudan, yana bawa Musulunci kariya a Sudan wanda ko Saudiyyah bata yin irinsa a Kasarta Yana daya daga cikin shugabannin Kasashen Musulunci a duniya wanda idan makiya Musulunci suka taba addinin Allah da Musulmai yake fitowa yayi magana, Kasar Iran daular masu bin addinin shi'ah sun taba yin mummunan batanci ga Sahabban Annabi (SAW) guda biyu Abubakar da Umar, a ranar ya kori Ambasadar Kasar Iran, kuma yasa aka rushe embassy na Iran dake Sudan, aka gina Sabon Masallaci a gurin, aka sanya wa Masallacin sunan Abubakar da Umar wato sunan Sahabban Annabi (SAW) Lokacin Shugaba Umar Albashir babu gidan sayar da giya a Sudan, babu gidan karuwai a Sudan, babu gidan caca da sauran guraren sabon Allah, mata basa shiga harkokin shugabanci, to wannan kariyar da ya bawa Musulunci,

Saudiyya Ta Kwashe ’Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Zuwa Kasarta

Image
Gwamnatin kasar Saudiyya ta kwashe wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a yakin da ya barke a Sudan zuwa kasarta. Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Zubairu Dada, ya ce Saudiyya ta tura jiragen ruwa da suka kwashe ’yan Najeriya zuwa birnin Jeddah na kasarta, bayan barkewar yaki a Sudan. Ma’aikatar ta ce daga bisani za a maido da ’yan Najeriyan da aka kai Saudiyya gida, kuma gwamnatin Tarayya na kokarin ganin cewa babu dan Najeriya ko daya da ya rage a Sudan kafin cikar wa’adin awa 72 da bangarorin da ke yaki da juna suka bayar na tsagaita wuta. Ta bayyana cewa a kokarinta na kwashe ’yan Najeriya da suka makale bayan barkewar yakin, Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliya 552 kan daukar hayar motocin da za su fitar da su zuwa iyakar Sudan da kasar Masar. Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyema, ya ce an dauki hayar bas-bas 40 da za su kwashi ’yan Najeriya daga Khartoum, babban birnin Sudan zuwa iyakar kasar Masar da ke Aswan, inda za su hau jirgi zuwa gi

Wayar salula ce ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89

Image
Rundunar sojin Rasha ta ce, akwai yiwuwar sojojinta sun yi amfani ne da wayoyin salula wadanda suka bai wa takwarorinsu na Ukraine damar gano matsuguninsu har suka kai musu farmakin da ya kashe 89 daga cikinsu. Sai dai tuni Rashawa suka fara mayar wa da rundunar sojin martani da suka ce, ta fadi haka ne domin wanke kanta daga zargin sakaci. Hatta masharhanta da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin sun ce, watakila ma adadin sojojin da suka mutun ya zarta 89. Asarar sojoji 89, ita ce mafi girma da Rasha ta ce ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Ukraine a cikin watan Fabairun bara. Sojojin na Rasha sun mutu ne sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar musu a Makiivka da ke yankin gabashin Ukraine, inda Rasha ta mamaye. (RFI)