Kuna Da Rawar Takawa Wajen Gudanar da Harkokin Filaye - Kwamishinan Kasa Ga Kwamitin Majalisa Kan Filaye
Kwamishinan kasa da tsare-tsare na Jiha, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da kwamitin majalisar dokokin jihar kan filaye domin inganta harkar filaye a jihar. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, Murtala Shehu Umar ya sanyawa hannu, yace Kwamishinan ya bayyana haka ne a yau (Juma’a) a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban da mambobin kwamitin majalisar dokokin jihar a kan filaye a ofishinsa. Ya ce tun da ya hau kan karagar Shugabanci ya ci gaba da yin aiki don gyara matsaloli da kalubalen da ke gaban ma’aikatar da kuma kawo cikas ga gudanar da harkokin mulki mai inganci a jihar. Don haka ya yi kira gare su da su ba shi goyon baya da hadin kai a kan hakan domin a matsayinsu na mambobin kwamitin kula da filaye suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen gyara harkokin mulki. Kwamishinan ya sanar da kwamitin cewa ma’aikatar na da kwararrun daraktoci kuma sun yi alkawarin ba shi dukkan goyon bay...