Search This Blog

Showing posts with label Hedikwatar 'Yan sanda. Show all posts
Showing posts with label Hedikwatar 'Yan sanda. Show all posts

Saturday, 14 January 2023

LABARI DA DUMIDUMINSA : Gobara ta tashi a Hedikwatar 'yan sanda ta Kano

Hedkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai a karamar hukumar Nasarawa, tana cin wuta, inda ake zargin ta kona ofisoshi da muhimman bayanai da dama.

 Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce tuni ta tura jami’an ta wurin da lamarin ya faru domin dakile gobarar da ta tashi a ginin bene mai hawa daya na rundunar.

 Rahotanni da basu tabbata ba sun nuna cewa gobara ta tashi ne a saman benen, Inda ta kama ko’ina amma banda ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda.


Ko da Majiyarmu ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar hannu, mun sami wayarsa a kashe har lokacin haษ—a wannan rahoton, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Clerics Call, Citizens Cheer: Kano Rallies Behind Muhuyi's Anti-Drug Task Force - By Abba Anwar

Politics apart, if there is anything non-political that can open corridor of victory for the Governor of Kano State,...