Posts

Showing posts with the label DMO

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa Naira Tiriliyan 46.25 - DMO

Image
Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 46.25 a watan Disamban 2022. A wata sanarwa a ranar Alhamis, DMO ya ce an samu karin sama da Naira tiriliyan bakwai daga abin da kasar ta mallaka a shekarar 2021. Kano: Ba zan rika yi wa gwamnatin Abba katsa-landan ba – Kwankwaso Masari: Tinubu na bukatar addu’a “Jimillar Bashin Jama’a wanda ya kunshi bashin cikin gida da na kasashen waje na Gwamnatin Tarayya da kananan hukumomi daga (Gwamnatin Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya), ya kai Naira Tiriliyan 46.25 ko kuma dala biliyan $103.1, kwatankwacin adadin ranar 31 ga watan Disamba, 2021, na Naira tiriliyan 39.5 wanda ya yi daidai dad ala biliyan $95.77. “Ta fuskar hada-hadakuwa, jimillar bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 27.55 daidai da dala biliyan $61.42, yayin da jimillar bashin waje ya kai Naira tiriliyan 18.7t daidai da dala biliyan $41.6. Ofishin ya bayyana cewa dalilan da suka sa aka kara samun yawan bashin