Gwamnan Jihar Kano Ya Ware Naira Biliyan Biyar Domin Biyan Kudaden 'Yan Fansho A Karo Na Biyu
...... Yace Gwamnatinsa Tana Kokarin inganta Jin Dadin Ma'aikata da 'Yan Fansho Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuduri aniyar samar da kyakkyawan yanayin rayuwa mai dorewa ga wadanda suka yi ritaya bayan aiki, inda ware karin naira biliyan biyar domin raba kashi na biyu na kudin fansho ga ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jihar Kano karo na goma sha hudu da ya gudana a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin Kano. Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta fitar da naira biliyan shida domin biyan dubban ‘yan fansho da ba su samu hakkokinsu ba a tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta shude. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an biya wadannan kudade ne domin tallafa wa wadanda suka yi ritaya da kuma sanya farin ciki a rayuwarsu, domin da y