Posts

Showing posts with the label Takardun Kudi

Dan Jarida Ya Mutu Yana Tattakin Zuwa Wurin Aiki Saboda Karancin Takardun Kudi

Image
  Wani fitaccen dan jarida da ke aiki a gidan rediyon Ibadan, ya riga mu gidan gaskiya a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki a safiyar wannan Asabar din. Ma’aikacin jaridar wanda aka fi sani da Baba Bintin, ya yanke jiki ne ya fadi matacce kamar yadda wakilinmu ya ruwaito. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne yayin da Baba Bintin ke hanyarsa ta zuwa gidan rediyon Fresh FM, inda zai gabatar da wani shiri tare da wasu takwarorinsa, Komolafe Olaiya da Olalomi Amole a yankin Challenge da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Baba Bintin dai ya shahara wajen gabatar da shirin bayyana farashin kayayyaki da ranakun cin kasuwannin yau da kullum a fadin jihar da kewaye. Rahotanni sun tabbatar da cewa karar kwana ta cimma Baba Bintin yayin da yake tattaki tun daga unguwarsu ta Amuloko zuwa Challenge sanadiyyar rashin tsabar kudi a hannu da zai biya masu ababen hawa na haya. Jama’a a Najeriya na ci gaba da babatu kan halin kunci da suka shiga tun bayan sauya fasalin takardun kudi da Babban Bankin Kasar CB

Kotun Ƙolin Ta Dakatar Da Gwamnatin Najeriya Dga Aiwatar Da Wa'adin Amfani Da Tsofaffin Kudi

Image
Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar. A baya dai CBN ya saka 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauya wa fasali. Jihohin arewacin ƙasar uku, waɗanda suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin. A hukuncin wucin-gadin da suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar. Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar su jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrair