Posts

Showing posts with the label Yaki da Cin Hanci

Ba Zamu Lamunci Yi Mana Katsalandan A Ayyukanmu Ba - EFCC

Image
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi kira ga jama’a  cewa laifi ne a hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. A sanarwar da Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar,  Dele Oyewale  ya sanyawa hannu, yace Sashi na 38(2)(a(b) na dokar kafa hukumar EFCC ya sanya laifin hana jami'an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. Masu laifi suna fuskantar daurin kurkuku na kasa da shekaru biyar. Wannan gargadin ya zama dole bisa ga yadda mutane da kungiyoyin da Hukumar ke bincike ke kara ta'azzara na daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar 'yan baranda domin dakile ayyukan EFCC. A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan tada zaune tsaye domin gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana É—aukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni. Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba domin kuw

Batan Sama Da Naira Biliyan Hudu : Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Ta Kama Babban Wanda Ake Zargi

Image
Inuwa, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar (Association of Compassionate Friends) kuma shi kadai ne ke sanya hannu kan asusun ajiyar wani kamfani mai suna Limestone processing Link da aka fi amfani da shi wajen karkatar da abin da aka gano. A sanarwar mai dauke da sa hannun mai bawa Shugaban Hukumar shawara kan harkokin yada labarai, Kabir Abba Kabir, tace an kama shi ne bayan da ya fasa rumfunan adana kayayyaki da aka kwace bisa ga sashe na 40 na Dokar Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta 2008 (kamar yadda aka gyara) wani mataki wanda kuma ya samu izini bisa umarnin kotu. An kama shi ne dangane da zargin karkatar da kudade da karkatar da kudade ko kuma mayar da kudaden gwamnatin jihar Kano na sama da naira biliyan hudu da aka tura wa tallafin kamfanin noma na Kano. Haka zalika, Bala Inuwa Muhammad wanda ya rattaba hannu a kai shi da mahaifinsa suka karkatar da kudaden da suka kai biliyan uku da miliyan dari biyu da saba’in da biyar da miliyan dari s