Posts

Showing posts with the label Sanata Barau Jibrin

Sanatoci 62 Sun Amince Da Barau Jibrin Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Image
A daidai lokacin da ake gudanar da sauye-sauye a zaben shugaban majalisar dattijai karo na 10, zababbun sanatoci 62 cikin 109 sun amince da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano a matsayin shugaban majalisar dattawa. Wani Sanata mai wakiltar Arewa maso Yamma kuma na hannun damar Jibrin ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa da suka yi da sanyin safiyar Talata a Abuja. Ya bayyana cewa kawo yanzu Zababbun Sanatoci 62 sun amince da Sanata Jibrin kuma 46 daga cikinsu sun halarci taron na dare a otal din Transcorp. Taron dai ya ta’allaka ne da dabarun hada kan sauran Zababbun Sanatoci domin hada hannu wajen ganin Sanata Jibrin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa na 10. Zababbun ‘yan majalisar, sun nuna adawa da nadin Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa. Mun san cewa Tinubu ya fi son Akpabio ne kawai don É—aukar Kiristoci a Najeriya, ba wai don cancanta ko gudunmawar da ya bayar don nasarar jam'iyyar ba. Sai dai abin takaici Akpabio ba zai iya tafiyar da harkokin ...