Posts

Showing posts with the label Wahalar Man Fetur

2023PDP Ce Ta Haifar Da Wahalar Man Fetur A Najeriya – Tinubu

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya ce dillalan man da PDP ta bai wa lasisi zamanin mulkinta ne ke boye fetur yanzu a Najeriya. Tinubu ya kuma ce magoya bayan PDPn da jam’iyyar ta bai wa lasisin zamanin mulkinta ne ke yin hakan saboda dalilan siyasa da kuma haddasa dogayen layuka a gidajen mai. Idan muka je saro kaya da tsoffin kudi ba a karba – ’Yan kasuwar Gombe ‘Duk Shugaban Kasar da zai zo zai fuskanci kalubale irin na Jonathan da Buhari’ Tinubu ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zabensa da ya gudanar a Jihar Binuwai ranar Alhamis. Ya ce, PDP Jam’iyya ce ta ruruta wutar talauci ce, musamman idan aka yi la’akari da yadda ’yan Najeriya ke shan bakar wahala a yanzu. Sun bai wa magoya bayansu lasisin da yanzu ya haifar da dogayen layuka na jabu a gidajen mai. PDP haka ya ishe ku fa!” Ya kuma ce rashin sanin doka ne ya sanya abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, ya ce kasuwancin sufuri yake a lokacin da yake aiki da Hukumar Hana Fasakwauri ta ...