Kuskuren Shekara 24 Ne Ya Jefa Najeriya Halin Da Ta Ke Ciki — Kwankwaso

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kuskuren da shugabannin baya suka yi a shekaru 24 da suka shude ne ya jefa Najeriya cikin tsaka mai wuyar da ta ke ciki a yanzu. 

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano, ya bayyana haka ne a Landan yayin da yake amsa tambayoyi a ‘Chatnam House’ game zaben Najeriya na 2023.

’Yan takarar Gwamnan Kano sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya
Dattijuwar da ta fi kowa tsufa a duniya ta rasu tana da shekara 118
A cewarsa, “Za mu iya alakanta kowane irin abu da ake zargin su ne ke da alhakin halin da muke ciki, tun daga annobar Kwarona zuwa koma bayan tattalin arzikin duniya da sauransu.

“Amma a ni a ganina, mun fada halin da muke ciki ne saboda kuskuren da mutanen da aka dora wa alhakin mulkin Najeriya suka tafka a cikin shekaru 24 da suka gabata.”

Kwankwaso wanda kuma tsohon Ministan Tsaron Najeriya ne, ya lissafa manyan matsaloli da kasar nan ke ciki da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, hauhauwar farashin kayayyakin masarufi da kuma rashin isassun kayan aikin kiwon lafiya.

A cewarsa ragowar sun hada da rashin tsari mai kyau game da ilimi, cin hanci da rashawa, satar danyen mai da sauransu.

Kwankwaso ya ce ya shirya yin takarar shugaban kasa ne saboda ya gano wuraren da tsofaffin shugabannin kasar nan suka tafka kuskure, kuma ya ce jam’iyyarsa ta shirya gyara wadannan kurakuran.

“Mun shirya tsaf, kuma muna da tsarin da zai ciyar da Najeriya gaba tare sa warware kowace irin matsala da aka bari.”
(AMINIYA) 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki