Posts

Showing posts with the label Labbo

Gwamna Umar Namadi Ya Nada Sabon Darakta Janar Na Hukumar Alhazai Ta Jigawa

Image
Gwamna Malam Umar A. Namadi ya amince da nadin Ahmed Umar Labbo a matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa na tsawon shekaru hudu. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim. Sanarwar ta ce nadin Labbo a matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa an yi shi ne bisa cancanta Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, Ahmed Umar Labbo ya yi aiki a matsayin Darakta aiyuka na hukumar kuma an daukaka shi zuwa matsayin babban sakataren hukumar a ranar 20 ga Maris, 2023 bisa la’akari da kwarewarsa da kuma tarihin aikinsa. “Saboda haka, muna fatan wanda aka nada zai tabbatar da amincewar da aka yi masa, ya kuma yi iya kokarinsa wajen ci gaban jihar Jigawa,” in ji SSG. Sanarwar ta bayyana cewa, nadin zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Janairu, 2024