Posts

Showing posts with the label Zargi

Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa

Image
Gwamnatin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan zargin babban cin amana da kuma zagon ƙasa ga sha’anin tsaron ƙasar. Masu juyin mulkin sun ce sun tattara hujjojin da za su yi amfani da su wajen gurfanar da Bazoum da kuma waɗanda suka kira muƙarrabansa na cikin gida da na ƙasashen waje. Ministan Matasa da Wasanni, Kanar-Manjo Amadou Abdraman ya sanar a talabijin a ranar Lahadi cewa za su gurfanar da Bazoum da muƙarraban nasa ne a cikin ƙasar Nijar da kuma gaban hukumomin da suka dace na duniya, kan babban cin amanar ƙasa da yin zagon ƙasa ga tsaron Jamhuriyar Nijar. Tun ranar 26 ga watan Yuli da sojojin suka yi wa Bazoum juyin mulki suke tsare da shi da matarsa da ɗansa a cikin gidansa. Shugabannin sojojin na iƙirarin cewa ba mamaye gidan nasa suka yi ba, domin kuwa yana ci gaba da mu’amala da sauran duniya, kuma likitansa na zuwa ya duba shi a kai a kai, yadda ya saba yi. Wani mashawarcin Bazoum ya tabbatar cewa a ranar Asabar

Majalisar Najeriya ta gayyaci ministoci kan bacewar gangunan danyen mai

Image
  Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin batar gangar danyen mai miliyan 48 a kasar ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar domin bayar da bahasi a game da wannan badakalar.  Da yake magana kan rashin girmama gayyatar da kwamitin ta ya yi wa Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu jami'an hukumomin gwamnatin kasar, Shugaban Kwamitin Binciken Hon. Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi Zainab Ahmed da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.   Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da karkatarwa zuwa China.     Ya ce a daya bangaren kuma, ana zargin Ministan Shari'a na kasar da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.    Ya kuma bayyana ce

DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

Image
  Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.   Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naɗi hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riƙa wallafa shi a shafukan sada zumunta.   Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar Taɓule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waɗanda ta kama.   “Cikin waɗannan saƙonnin masu haɗari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.   “Waɗanda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar. “Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukum