Hukumar DSS Ta Musunta Mamaye ofishin Gwaman Babban Bankin Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta mamaye harabar babban bankin Najeriya, a ranar Litinin, kamar yadda ake yada labarin a yanar gizo. Rundunar ‘yan sandan sirrin a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya ya fitar ta ce labarin karya ne. Idan dai za a iya tunawa a ranar Litinin din da ta gabata ne aka ga motocin a harabar babban bankin da ke Abuja. Hukumar ta DSS a cikin sanarwar ta ce jami’anta ba su yi yunkurin kama gwamnan na CBN ba.