Search This Blog

Showing posts with label Hawan Jini. Show all posts
Showing posts with label Hawan Jini. Show all posts

Saturday, 18 May 2024

Kashi 28.5 Na Kanawa Na Fama Da Hawan Jini — Kwamishinan Lafiya



A duk Nijeriya cutar hawan jini ta fi ƙamari a tsakanin al’umma Jihar Kano.


Gwamnatin Kano ta ce, kashi 28.5 cikin 100 na mutanen jihar masu shekaru tsakanin 30 zuwa 79 na fama da cutar hawan jini inda aka gano kusan kashi biyu bisa uku (60.7 cikin 100) sabbin waɗanda suka kamu da cutar.


Kwamishinan Lafiya na jihar, Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a bikin ranar hawan jini ta duniya na shekarar 2024 mai taken: “Ku Auna Hawan Jininku, Ku Daidaita Shi Domin Samun Rayuwa Mai Tsawo”.


Ya ce, “Hawan hawan jini ne babban abin da ke haifar da ɗimbin matsalolin lafiya kamar shanyewar ɓarin jiki, ciwon zuciya da ciwon ƙoda da sauransu.


“Yawancin mutanen da ke fama da hawan jini ba su san cewa suna ɗauke da cutar ba saboda ba a gani wasu alamominta.


“Sau da yawa, mutane sun fi fahimtar cewa suna ɗauke da cutar bayan sun kamu da ciwon zuciya ko shanyewar ɓarin jiki.

“Kimanin manyan mutane biliyan 1.28 masu shekaru 30 zuwa 79 a duniya suna fama da hawan jini.

“Sannan an kiyasta cewa adadin masu hawan jini a duniya zai ƙaru zuwa fiye da kashi 31 cikin 100 na mutanen duniya nan da shekarar 2025.


“A yanzu alƙaluman masu hawan jini a Najeriya ya kai kashi 27.6 cikin 100, inda a Jihar Kano, abin da ya fi ƙamari.

“A Jihar Kano, akasarin masu fama da cututtuka da ke da nasaba da zuciya sun samo asali ne daga hawan jini inda alƙaluman ya kai kashi 28.5 cikin 100 daga ciki, wanda daga ciki kusan kashi biyu bisa uku (kaso 60.7 cikin 100) a baya bayan aka gano suna fama da wannan matsala.”

Ya ƙara da cewa, a wani ɓangare na ayyukan tunawa da Ranar Hawan Jini ta Duniya na shekarar 2024, za a kafa cibiyar yi wa jama’a gwajin cutar hawan jini a Ƙaramar Hukumar Gwale da ke Kanon.
(AMINIYA)


Sunday, 7 May 2023

Yin Waya Fiye Da Minti 30 A Sati Na Kara Hawan Jini —Bincike


Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa karuwar cutar hawan jini da kashi 12.

Rahoton da Kungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya bukaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar Digital Health yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na kara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100.

Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda na’urorin zamani ke shafar lafiyar zuciya, ta ce hakan bai shafi yawan shekarun da mutun ya yi yana amfani da waya ko sanya waya a lasifika ba.

Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Aikin Likita tat Kudancin Guangzhou da ke kasa China, ya kara da cewa masu amfani da waya sun fi mara sa yi yiwuwar kamuwa da hawan jini da kashi 7 cikin 100.

Farfesa Qin ya a halin yanzu kusan biliyan 1.3 masu shekaru 30 zuwa 70 na da hawan jini, wadda ke iya kawo shanyewar barin jiki da kuma mutuwa farat-daya.

Masanin ya bayana cewa “Wayoyin hannu na fitar da maganadisun da ke kara hadarin kamuwa da hawan jini bayan wani lokaci.

“Duk da haka yanayin amfani da waya da ke kawo hawan jini ya bambanta a tsakanin masu kira ko amsawa, da kuma masu tura sakonni ko kuma yin wasanni da ita,” in ji Farfesa Qin.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...