Posts

Showing posts with the label Tawagar 'yanjaridu

Hajj 2024: Gwamnatin Kano Ta Nada Kakakin Mataimakin Gwamna Matsayin Wanda Zai Jagoranci Tawagar 'Yanjaridu A Hajin 2024

Image
Gwamnatin jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar yada labarai na aikin hajjin 2024. An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na kaddamar da Kwamitocin gudanar da aikin Hajji na shekarar 1445AH/2024 a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da ke cikin babban birnin jihar. Taron ya samu halartar ma’aikatan kafafen yada labarai da za su rika ba da labarin yadda ake gudanar da ibadar al’ummar Musulmi a duk shekara, wanda ke daukar dubban maniyyata daga Najeriya da ma sauran sassan duniya baki daya. Shuaibu, wanda a halin yanzu shi ne sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kware a harkar yada labarai da sadarwa. Ya kuma taba zama tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) Correspondents Chapel reshen jihar Kano, da kuma wakilin jaridar This Day. Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban tawagar kafafen yada labarai wani gagarumin ci gaba ne gabanin Hajjin 2024, kuma da