Posts

Showing posts with the label Bitar Alhazai

Hajj2024: Hukumar Alhazai Ta Jahar Kano Ta Bukaci Alhazai Da Su Guji Ficewa Daga Rukunin Da Aka Sanyasu

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya sake jaddada a yau muhimmancin alhazai wajen bin tsarin kungiya a yayin da ake ci gaba da gudanar da horaswa na yau da kullum a Cibiyar Musulunci ta Rano. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya jaddada cewa rukunin ko kuma kumgiya wani sabon umarni ne daga Hukumar Alhazai ta Saudiyya, wanda ke bukatar kungiyoyin mutane arba’in da biyar karkashin jagorancin mace daya namiji da daya. Ya kara jaddada wajabcin bin wadannan umarni na tashi daga Jidda har zuwa kammala aikin Hajji. Dangane da kudin guzuri  (BTA), ya bukaci alhazai da su guji sayayyar da ba dole ba, yana mai bayyana cewa, manufar wannan kudi shi ne biyan bukatar da ba zato ba tsammani ko na gaggawa. Alhaji Lamin Rabi’u, wanda ya samu wakilcin mamban hukumar kuma shugaban Kwamitin Malaman Bita na jihar, Sh

Hajjin Bana: Hukumar Alhazai Ta Kano Za Ta Ci Da Yin Bita A Wannan Makon Sakamakon Dage Ranar Zabe

Image
Sakamakon dage zabe da hukumar zabe ta kasa ta yi, hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano na sanar da Malaman Bita da Kuma Maniyyatan Jihar Kano cewa za'a ci gaba da yin Bitar mako mako a wannan satin wato Asabar da Lahadi 11 da 12 GA watan Maris ,2023 a Cibiyoyin Bita 16 da ke fadin Jihar Kano Sanarwar wacce Mataimakiyar Daraktar Ilmantarwa da wayar da kan Alhazai ta Hukumar Hadiza Abbas Sanusi ta fitar, ta yi kira ga dukkanin maniyyatan su halarci Cibiyoyin nasu domin akwai fa'ida mai yawa ga yin hakan 

Hajj2023: Hukumar Alhazai Ta Kano Za Ta Fara Gudanar Da Bitar Alhazai Ga Maniyyata Aikin Hajin bana

Image
Sakataren Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, shi ne ya bayar da wannan umarni ga dukkan Shugabanni da Malaman Bita, na Bitar mako-mako dake fadin jahar Kano  A sanarwar da Mataimakin Sakataren kwamitin malaman Bitar na Jaha, Malam Dahiru Kabiru Guringawa ya fitar, ta ce akwai shugaban kwamitin Bitar, Sheikh Haroon Muhd Sani Ibn Sina yace, za a fara gudanar da bitar ce daga ranar Asabar 4 ga watan Fabarairu na 2023 da karfe 10 na safe  Za a fara gudanar da Bitar ce a dukkanin Cibiyoyin bitar dake fadin jahar Kano.  A saboda sai sanarwar ta yi kira ga dukkanin Jami'an Alhazai na kananan hukumomi dasu tabbata sun sanarwa da dukkanin maniyyatansu don su halarta