Search This Blog

Showing posts with label Saudia. Show all posts
Showing posts with label Saudia. Show all posts

Monday, 30 October 2023

Gwamna Abba Kabir Ya Yi Bankwana Da Tagwayen Da suka hade Da Za Ayi Tiyatar Rabasu A Saudiyya

....Ya yabawa Masarautar Saudiya bisa kara kaimin agaji ga Kano

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yabawa masarautar Saudiyya karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdul'aziz kan daukar nauyin yi wa jarirai tagwaye a Kano tiyata a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a birnin Riyadh.

Da yake jawabi a lokacin da yake bankwana da iyayen tagwayen jarirai a filin jirgin sama na Aminu Kano, gwamnan ya bayyana irin alherin da Sarki Salman ya yi a matsayin wani aiki da Allah ya saka masa da ya dace a yi koyi da shi.

Gwamna Yusuf wanda ya yi addu’ar Allah ya dore da dankon zumuncin da ke tsakanin Kano da Masarautar Saudiyya, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na dawo da martabar da aka rasa a bangaren kiwon lafiya na jihar.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Gwamnan ya tuna cewa ba da dadewa ba Likitocin Saudiyya suna Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, domin kula da marasa lafiya da ke fama da ciwon zuciya da matsalar idanu kyauta.

Don haka ya yi addu’a ga jariran tagwayen da suka hade da juna don samun nasarar aikin tiyatar da aka yi musu sannan kuma suka dawo da rai a matsayin mutane biyu masu zaman kansu.

Da yake jawabi tun da farko, karamin jakadan Saudiyya a Kano, Sheikh Khalil Al'adamawi ya bayyana cewa, irin wannan shiri na nuni ne da yadda Saudiyyar ta himmatu wajen gudanar da ayyukan jin kai da kuma sadaukar da kai wajen taimakon mabukata.

Ya kuma kara da cewa, ana mika wannan karimcin ne ga mabukata ba tare da la’akari da kasarsu ko asalinsu ba, yana mai jaddada cewa masarautar Saudiyya ce kan gaba wajen samar da kayayyakin jin kai na kasa da kasa.

Daga nan ne karamin jakadan ya bayyana cewa za a kwantar da iyayen tagwayen da suka hade a birnin Riyadh, kuma za a ba su tsarin tallafi don samun kwanciyar hankali da taimako a tsawon tafiyar.

A nasa jawabin, mahaifin tagwayen da suka hada da, Malam Hassan Isa Kano ya bayyana matukar godiyar iyalansa ga mai kula da masallatai biyu masu tsarki, Salman Bin Abdulaziz bisa daukar nauyin yi wa tagwayen, Hassana da Husaina aikin tiyata, yana mai addu’ar Allah ya jikansa. don saka masa da iyalansa da jannatul Firdausi.

Ya kuma yabawa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa kauna da kulawar da ya nuna musu tare da ba su lokaci domin yi musu bankwana a filin jirgin sama a yau.


Thursday, 6 July 2023

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar Saudiyya ta ce, yanayin zafi a gobe Juma’a, zai kai daraja Hamsin na tsananin Zafi.

Saboda wannan zafin yanayin, Gwamnatin Saudiyya na bada shawarar cewa Alhazai da suyi Sallar Jumma’ah a Masallatan da suka fi kusa da gidajensu don kaucewa shiga tsananin rana. 

Don haka Ma’aikatar Aikin Hajji ta Kasar Najeriya na kara jaddada ayi anfani da wannan nasihar ta yin Salla a Masallatai Mafiya kusa da Masaukan Alhazanmu.

Sanarwar wacce babban jami'in hukumar NAHCON dake Makkah, Dr Ibrahim Muhammad Sodangi ya sanyawa hannu, ta yi fatan Alhazan zasu yi amfani da wannan shawara ta kwararru da aka domin kaucewa shiga babbar matsala 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...