Kotu ta ɗaure Ekweremadu shekara tara a gidan yari
An yanke wa wani hamshaƙin ɗan siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗauri a gidan yari bayan kotu a Birtaniya ta same su da laifi kan yunƙurin safarar sassan jikin ɗan'adam. Kotun ta yanke musu hukuncin ne tare da wani likita "mai shigar musu tsakani" bayan sun kai wani matashi Birtaniya daga Lagos. Yanzu dai, Sanata Ike Ekweremadu zai shafe kusan shekara goma a gidan yarin Birtaniya. Sanatan mai shekara 60, da mai ɗakinsa Beatrice 'yar shekara 56, sun so a cire wa matashin sashen jikinsa ne da nufin dasa wa 'yarsu Sonia 'yar shekara 25, kamar yadda ma'auratan suka bayyana wa Kotun Old Bailey An kuma samu "mai shiga tsakani" Dr Obinna Obeta da matar sanata Ekweremadu, Beatrice, da laifi Tun da farko kotu ta samu ma'auratan da likita Dr Obinna Obeta, mai shekara 50, da laifin haɗa baki don ci da gumin mutumin ta hanyar cire ƙodarsa. Ita ce shari'a ta farko a ƙarƙashin dokokin haramta bautar zamani. Yadda a...