Search This Blog

Showing posts with label Gwamnati. Show all posts
Showing posts with label Gwamnati. Show all posts

Wednesday, 31 May 2023

Za Mu Yi Fito-Na-Fito Da Gwamnati Kan Cire Tallafin Man Fetur - Kungiyar Kwadago

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan yunkurin da sabon shugaban Najeriyar ke yi na janye tallafin mai.

Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al'umma a cikin wahala.

Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa BBC cewa shugaban Najeriyar ya yi hanzarin sanar shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

"Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu", in ji shi.


Kungiyar ta yi ikirarin a cikin sa'o'i bayan sanarwar shugaban kasa alummar kasar sun tsinci kansu cikin wani hali na tsaka mai wuya saboda an fuskanci karancin man fetur a wasu sassan kasar da karin farashin mai inda a wasu wurare gidajen mai farashin man fetur din ya karu da kashi 300 cikin 100.

Mahukuntan kasar sun sha ikirarin cewa wasu tsiraru ne ke amfana da tallafin man, don haka yakamata a cire shi .

To sai dai NLC ta yi watsi da haka kamar yada Kwamarade Nasir Kabir ya bayyana:

"Duk wannan magana ne ina tabbatar maka tatsuniya ce, ba mu gamsu da shi ba, ai maganar gaskiya shi ne me ya sa su gwamnatin da ta shigo da ke son ta janye wannan tallafi, da mun zauna mun nuna mu su aubuwan da ke kasa, sai su gane cewa mun fi su gaskiya sai su fasa", in ji shi.

Kungiyar kwadagon ta ce tana adawa da wannan mataki na shugaba Tinubu kuma ta nemi gwamnati da ta janye shirin cikin gaggawa.

NLC ta kuma yi ikirarin cewa abubuwan da wannan mataki zasu haifar za su yi illa ga fanin tsaro da walwalar jama’a.

Hon Abubakar Yunus ɗan majalisar wakilai daga Gombe ya shaidawa BBC cewa dawainiyar ta fi karfin gwamnati, kuma talakawa ba sa amfana da tallafin man.

"Ai mun jima muna kira ga tsohon shugaban kasa Muhamadu Buhari da lallai ya janye tallafin.

"Mun kawo korafe korafe a kan cewa tallafin nan in banda cutar da jama'ar da suke kuka a yanzu, ai gara ma a cire shi.

"Da sun san badakalar da babakere da ake yi mu su a wannan harka ta subsidy,…ko da za su yi azumin wata guda da sun amince a cire shi".

Batun janye tallafin dai a yanzu shi kowa ke tattaunawa a kai, fatan 'yan Najeriya dai shi ne samun rangwame daga hauhawa farashin da wasu ke ganin babu mamaki ya karu da wannan sabon tsari.

BBC Hausa 

Sunday, 23 April 2023

Sarkin Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Wata Hanyar Da Al'uma Zasu Samu Saukin Rayuwa

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al'amuran rayuwarsu.

Ya kuma tunasar da al'uma shirin gwamnati na Kidayar al'uma da za'a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al'uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar.

Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu'oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al'uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikace da gwamnati takeyi tana yin domin al'uma.

Ya godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da ilimi, Noma, Masana'antu da gina tituna da Gadoji inda yace wannan yasa an samu cigaban habaka tattalin arzikin jihar nan da masu saka hannun jari da kuma shigowar masu yawon bude idanu.

Daganan sarkin ya godewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul tareda yi masa addu'a da fatan alheri samun matsayi na gaba sakamakon gabatowar karshen wa'adin mulkinsa.

Da yake Jawabi Mukaddashin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya godewa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR bisa wannan ziyara da yakawo gidan Gwamnati ta Hawan Nassarawa inda yace wannan ziyara ce ta al'ada da aka gada daga wajan magabata.

Dr. Gawuna ya godewa al'umar jihar Kano bisa hadin kai da goyon baya da suka baiwa gwamnatinsu har na tsawon shekara 8 da sukayi suna mulki, Yana mai kira a garesu dasu cigaba da kasancewa masu bin doka da oda a kowanne lokaci.

Tuesday, 11 April 2023

Rashin Lafiyar Buhari Ta Kawo Wa Gwamnatinsa Cikas —Adesina

Mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce rashin lafiyar da Shugaban Kasa ya yi a 2017 ta janyo wa gwamnatinsa nakasun aiki na watanni takwas a mulkinsa.

Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zanta wa a gidan talabijin na Channels.

Adesina, wanda ya bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yayin zantawar, ya ce shugaban ya shafe watanni takwas yana jinya a Ingila a 2017.

“Lokacin da ya soma rashin lafiya a watan Janairun 2017, ya dawo a watan Maris, ya sake komawa a watan Afrilu kuma bai dawo ba sai 19 ga watan Agusta.


“Wannan jinya ta dauki wata takwas ba tare da yana aiwatar da komai ba. Tabbas, babu wanda zai so hakan amma abun farin ciki shi ne daga baya ya samu lafiya.”

Sai dai ya ce duk da wannan koma baya da aka samu, shugaba Buhari zai bar kasar nan cikin nagarta fiye da yadda ya same ta.

Adesina ya bayyana cewa a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya karbi mulki, kananan hukumomi 17 na hannun ‘yan ta’adda, amma daga bisani gwamnatinsa ta kwato su bayan karbar mulkin.


Game da tattalin arziki kuwa, ya yi nuni da cewa a yanzu Najeriya na da karfin tattalin arziki iri daban-daban a sakamakon kokarin da gwamnatin Buhari ta yi.


Hadimin ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Buhari ta fuskanta baya ga rashin lafiyar da ya shafe wata takwas yana yi, ya yi manyan ayyuka na a zo a ga ni.

Idan ba a manta ba, a baya-bayan nan masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewar Buhari ya gaza cika alkawarin da ya yi na cire miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci.
AMINIYA 

Monday, 10 April 2023

Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa a Salla

 


Gwamnatin Algeria ta karrama limamin nan, Imam Walid Mehsas wanda kyanwa ta dare jinkinsa a daidai lokacin da yake jagorantar Sallar Taraweeh, inda cikin tausasawa ya yi ta shafar kwanyar wadda ta sunbace shi kafin daga bisani ta sauka daga jikinsa don ratsin kanta.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ne ya nuna yadda Imam Walid ya mu’amalanci kwanyar cikin kyawun yanayi, lamarin da ya kayatar da jama’a da dama hatta wadanda ba Musulmai ba daga sassan duniya.

Limamin ya sha yabo da jinjina, yayin da manyan kafafen yada labarai na duniya suka yi ta yada wannan labarin.

Yanzu haka gwamnatin Algeria ta gayyace shi tare da shirya masa taron liyafa na musamman, inda Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar, Dr. Youssaf Belmahdi ya yaba masa kan wannan kyakkyawar dabi’ar da ya nuna wa dabba.

RFI

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...