Yanzu-yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin nade-naden mukamai
A kokarinsa na kara baiwa jihar Kano karfin gwiwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nada karin masu ba da shawara na musamman da sauran shugabannin hukumomin gwamnati. A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mai magana da yawun gwamnan ya yi ishara da wadanda aka nada kamar haka: 1. Farfesa Ibrahim Magaji Barde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR). 2. Dr. Abdulhamid Danladi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasashen waje II 3. Injiniya Bello Muhammad Kiru, mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa. 4. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) ya sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni. 5. Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, Injiniyan Ruwa da Gine-gine (WRECA). 6. Hon. Haka kuma Baba Abubakar Umar an dauke shi ne daga mai ba shi shawara na musamman ga babban sakataren gudanarwa, hukumar kula da...