Posts

Showing posts with the label Gwamnan Adamawa

INEC Ta Bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jahar Adamawa

Image
Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama. Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861. Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788. Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu. Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage. A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen cikin wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20. An sake kaɗa ƙuri'u ne a tashoshin zaɓe 69. Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa ya nuna cewa 'yar takarar ...